Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 6:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Don haka, ku ne na fari da za a sa suyi ƙauraBukukuwanku da shagulgulanku zasu ƙare.

8. Ubangiji kansa ne ya rantse.Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,“Ba na son girmankai na jama'arIsra'ila.Ba na son fādodinsu.Zan ba da birnin da dukan abin dayake cikinsa ga abokan gābansu.”

9. Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.

10. Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?”Sai a amsa, “A'a.”Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Amos 6