Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 6:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannanrana ta masifa,Amma ga shi, goyon bayan hargitsikuke ta yi,Ta wurin ayyukanku.

4. Taku ta ƙare, ku da kuke kwancekan gadajen hauren giwa,Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayenkujerunku,Ku ci naman maraƙi da na rago.

5. Kukan so ku tsara waƙoƙi kamaryadda Dawuda ya yi,Ku raira su da garayu.

6. Da manyan kwanoni kuke shanruwan inabi,Ku shafe jiki da mai mafi kyau,Amma ba ku yin makoki sabodalalacewar Isra'ila.

7. Don haka, ku ne na fari da za a sa suyi ƙauraBukukuwanku da shagulgulanku zasu ƙare.

8. Ubangiji kansa ne ya rantse.Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,“Ba na son girmankai na jama'arIsra'ila.Ba na son fādodinsu.Zan ba da birnin da dukan abin dayake cikinsa ga abokan gābansu.”

9. Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.

Karanta cikakken babi Amos 6