Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 6:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Taku ta ƙare, ku da kuke zamansakewa a Sihiyona,Da ku da kuke tsammani kunazaman lafiya a Samariya,Ku da kuke manyan mutaneNa wannan babbar al'umma taIsra'ila,Waɗanda jama'a suke zuwa a gare suneman taimako!

2. Ku je ku duba a birnin Kalne.Sa'an nan ku zarce zuwa babbanbirnin Hamat,Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa.Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne?Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya finaku?

3. Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannanrana ta masifa,Amma ga shi, goyon bayan hargitsikuke ta yi,Ta wurin ayyukanku.

4. Taku ta ƙare, ku da kuke kwancekan gadajen hauren giwa,Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayenkujerunku,Ku ci naman maraƙi da na rago.

5. Kukan so ku tsara waƙoƙi kamaryadda Dawuda ya yi,Ku raira su da garayu.

6. Da manyan kwanoni kuke shanruwan inabi,Ku shafe jiki da mai mafi kyau,Amma ba ku yin makoki sabodalalacewar Isra'ila.

7. Don haka, ku ne na fari da za a sa suyi ƙauraBukukuwanku da shagulgulanku zasu ƙare.

Karanta cikakken babi Amos 6