Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 5:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku kasa kunne, ku jama'arIsra'ila, ga waƙar makoki da zan yia kanku.

2. Isra'ila ta fāɗi,Ba kuwa za ta ƙara tashi ba.Tana fa kwance a ƙasa,Ba wanda zai tashe ta.

3. Ubangiji ya ce,“Wani birnin Isra'ila ya aika da sojadubu,Ɗari ne kaɗai suka komo,Wani birni kuma ya aika da soja ɗarine,Amma goma kaɗai suka komo.”

4. Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila,“Ku zo gare ni, za ku tsira.

5. Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba.Kada ku yi ƙoƙarin nemana aBetel,Gama Betel lalacewa za ta yi.Kada ku tafi Gilgal,Gama an ƙaddara wa jama'arta suyi ƙaura.”

6. Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira.Idan kuwa kun ƙi,Shi zai babbaka jama'ar YusufuKamar yadda a kan babbaka dawuta.Wuta za ta ƙone jama'ar Betel,Ba kuwa mai kashe wutar.

7. Abin tausayi ne ku da kuke ɓatashari'a,Kuna hana wa mutane hakkinsu.

8. Ubangiji ne ya yi taurarinKaza da 'ya'yantaDa mai farauta da kare.Ya mai da duhu haske,Rana kuwa dare.Shi ya kirawo ruwan teku yabayyana,Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa.Sunansa Ubangiji ne.

9. Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,Da a kan birane masu garu.

10. Kun ƙi wanda ya tsaya a kanadalci,Da mai faɗar ainihin gaskiya a gabanshari'a.

Karanta cikakken babi Amos 5