Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 4:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya yi bagade na tagulla, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin, tsayinsa kuwa kamu goma.

2. Ya yi kwatarniya kewayayyiya ta zubi, kamu goma daga gāɓa zuwa gāɓa, tsayinsa kuwa kamu biyar ne, da'irarsa kuwa kamu talatin.

3. A ƙashiyar kwatarniya akwai siffofin bijimai kamu goma kewaye da ita har jeji biyu. Gaba ɗaya aka yi zubinsu da na kwatarniya.

4. Kwatarniya tana bisa bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar gabas, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. Kwatarniya tana bisa bijiman, gindin kowannensu yana daga ciki.

5. Kaurin kwatarniya taƙi guda ne, bakinsa kamar bakin finjali ne, kamar kuma siffar furen bi-rana. Kwatarniya kuwa tana iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa.

6. Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne.

7. Sa'an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu.

8. Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.

9. Sa'an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla.

10. Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.

Karanta cikakken babi 2 Tar 4