Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 36:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.

18. Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.

19. Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.

20. Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na 'ya'yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,

21. don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba'in, ta kiyaye asabatai.

22. Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

Karanta cikakken babi 2 Tar 36