Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 36:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan'uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.

11. Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.

12. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.

13. Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra'ila.

14. Dukan manyan firistoci da sauran jama'a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al'ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.

15. Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama'arsa da wurin zaman zatinsa.

16. Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba'a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba'a, sai Ubangiji ya husata da jama'arsa don abin ya kai intaha.

Karanta cikakken babi 2 Tar 36