Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 35:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa.

2. Ya sa firistoci a matsayinsu, ya ƙarfafa su a hidimar Haikalin Ubangiji.

3. Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila.

4. Ku karkasa kanku bisa ga gidajen kakanninku ƙungiya ƙungiya, ku bi bayanin Dawuda, Sarkin Isra'ila, da na ɗansa Sulemanu.

5. Ku tsaya a Wuri Mai Tsarki, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin 'yan'uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa.

6. Ku yanka abin Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya wa 'yan'uwanku su yi bisa ga maganar Ubangiji ta hannun Musa.”

7. Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da 'yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne.

8. Da yardar rai manyan ma'aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama'ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma'aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku.

9. Konaniya kuma tare da Shemaiya da Netanel, 'yan'uwansa, da Hashabiya, da Yehiyel, da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, su suka ba Lawiyawa abin yin hadayar Idin Ƙetarewa, raguna da 'yan awaki dubu biyar (5,000), da bijimai ɗari biyar.

10. Sa'ad da aka shirya yin hidimar, firistoci suka tsaya a wurinsu, Lawiyawa kuwa suka tsaya bisa ga ƙungiyoyinsu, yadda sarki ya umarta.

Karanta cikakken babi 2 Tar 35