Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 34:12-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Mutanen fa suka yi aiki mai aminci tare da waɗanda suke lura da su domin su gabatar da aiki, wato Yahat da Obadiya, Lawiyawa, 'ya'yan Merari, maza, da Zakariya da Meshullam na wajen 'ya'yan Kohatawa, da waɗansu Lawiyawa da suke da gwanintar bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe.

13. Su ne shugabannin masu ɗaukar kaya, suke kuma nuna wa kowane ma'aikaci irin aikin da zai yi, waɗansu daga cikin Lawiyawa, magatakarda ne, da ma'aikatan hukuma, da masu tsaron ƙofofi.

14. Sa'ad da suke fitowa da kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya gāno littafin Shari'ar Ubangiji wanda aka bayar ta hannun Musa.

15. Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari'a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin.

16. Shafan kuma ya kai wa sarki littafin, sa'an nan ya faɗa wa sarki cewa, “Dukan abin da aka sa barorinka su yi suna yi.

17. Sai suka juye kuɗin da aka samu don Haikalin Ubangiji, suka miƙa wa masu lura da aikin, da ma'aikatan.”

18. Magatakarda Shafan kuwa ya faɗa wa sarki, ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta wa sarki littafin.

19. Da sarki ya ji irin maganganun da littafin ya faɗa, sai ya yayyage tufafinsa.

20. Sa'an nan sarki ya umarci Hilkiya, da Ahikan ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mika, da magatakarda Shafan, da Asaya baran sarki, ya ce,

21. “Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra'ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”

22. Hilkiya kuwa tare da waɗanda sarki ya aika suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, ɗan Harhas, mai lura da wurin ajiyar tufafi, tana zaune a Urushalima, a unguwa ta biyu. Suka faɗa mata saƙon sarki,

23. sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce in faɗa wa mutumin da ya aiko gare shi,

24. ‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la'anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza.

25. Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’

26. Amma a kan Sarkin Yahuza wanda ya aike ku ku tambayi Ubangiji, ga abin da za ku faɗa masa, ‘Ni Ubangiji, Allah na Isra'ila na ce, a kan maganar da ka ji,

27. da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa'ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.

28. Ga shi, zan kai ka wurin da kakanninka suke, a kabarinka a binne ka da salama, ba za ka ga dukan masifun da zan kawo wa wurin nan da mazaunansa ba.’ ”Sai suka isar da amsa wurin sarki.

Karanta cikakken babi 2 Tar 34