Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 32:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa'an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,

10. “Ga abin da Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya ce, ‘Ga me kake dogara, da har yanzu kuka dāge a cikin Urushalima, ga shi kuwa, yaƙi ya kewaye ta?

11. Ai, Hezekiya, ba ruɗinku yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi sa'ad da yake ce muku Ubangiji Allahnku zai cece ku daga hannun Sarkin Assuriya?

12. Ashe, ba wannan Hezekiya ba ne ya ɗauke masujadansa da bagadansa, ya kuma umarci Yahuza da Urushalima, su yi sujada a gaban bagade guda, a kansa ne kuma za su ƙona hadayu?

13. Ashe, ba ku san abin da ni da kakannina muka yi wa dukan jama'ar waɗansu ƙasashe ba? Gumakan al'umman waɗannan ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna?

14. Daga cikin dukan gumakan waɗannan al'ummai waɗanda kakannina suka hallakar da su sarai, ba wanda ya iya ceton jama'arsa daga hannuna, har da Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?

15. Yanzu fa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, ko ya ɓad da ku haka, kada kuwa ku gaskata shi, gama ba wani gunki na wata al'umma, ko wani mulki wanda ya taɓa ceton jama'arsa daga hannuna, ko kuma daga hannun kakannina. Wane Allah naku har da zai iya cetonku daga hannuna?’ ”

16. Barorinsa kuwa suka ƙara yin maganganun saɓo gāba da Ubangiji Allah da bawansa Hezekiya.

17. Ya kuma rubuta wasiƙu, ya zargi Ubangiji Allah na Isra'ila, ya yi maganar saɓo, yana cewa, “Kamar yadda gumakan al'umman sauran ƙasashe suka kāsa ceton jama'arsu daga hannuna, haka nan kuma Allahn Hezekiya ba zai iya ceton jama'arsa daga hannuna ba.”

18. Da babbar murya, da Yahudanci kuwa, suka yi ta yin magana da jama'ar Urushalima waɗanda suke kan garu, don a tsoratar da su, a kuma firgita su, don su ci birnin.

19. Suka yi ta magana a kan Allah na Urushalima, kamar yadda suka yi magana a kan gumakan al'ummai, wato aikin hannuwan mutane.

Karanta cikakken babi 2 Tar 32