Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 32:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan waɗannan abubuwa, da waɗannan ayyukan aminci, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa Yahuza yaƙi, ya kafa sansani kewaye da garuruwa masu garu, yana zaton zai ci su da yaƙi su zama nasa.

2. Da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo da nufin ya yi yaƙi da Urushalima,

3. sai ya yi shawara shi da jarumawansa da manyan mutanensa, su datse ruwan da yake fitowa daga maɓuɓɓugar da suke bayan birni, suka kuwa taimake shi.

4. Don haka mutane da yawa suka taru suka daddatse dukan maɓuɓɓugai da rafuffuka da suke gudu cikin ƙasar, suna cewa, “Bari mu hana sarakunan Assuriya samun ruwa idan sun iso Urushalima.”

5. Sai ya kama aiki gadangadan, ya sāke gina dukan garukan da suka rushe, ya gina hasumiya a kai, ya kuma gina wani garu bayan wannan, ya ƙara ƙarfin Millo a birnin Dawuda, ya kuma yi makamai na yaƙi da garkuwoyi masu yawan gaske.

6. Sai ya sa manyan sojoji su shugabanci jama'a. Su tattaro su gare shi a dandalin ƙofar birni, ya yi musu magana ta ƙarfafawa ya ce,

7. “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda Sarkin Assuriya, da dukan taron da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.

8. Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.

9. Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa'an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,

10. “Ga abin da Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya ce, ‘Ga me kake dogara, da har yanzu kuka dāge a cikin Urushalima, ga shi kuwa, yaƙi ya kewaye ta?

Karanta cikakken babi 2 Tar 32