Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 29:28-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Dukan taron suka yi sujada, mawaƙa suna ta raira waƙa, masu ƙahoni suka yi ta busa. Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa.

29. Bayan da an gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada.

30. Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.

31. Hezekiya kuwa ya amsa ya ce, “Yanzu dai kun tsarkake kanku ga Ubangiji. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a Haikalin Ubangiji.” Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, dukan waɗanda suka yi niyya kuwa suka kawo hadayu na ƙonawa.

32. Jimillar hadayu na ƙonawa waɗanda taron suka kawo, su ne bijimai saba'in, da raguna ɗari, da 'yan raguna ɗari biyu, waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Ubangiji.

33. Abubuwan da aka keɓe kuwa bijimai ɗari shida ne, da tumaki dubu uku (3,000).

34. Amma su firistoci kima ne, don haka sun kāsa fiɗa dukan dabbobin da za a miƙa su hadaya ta ƙonawa. Sai 'yan'uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu.

35. Banda hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi, akwai kuma kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowace hadaya ta ƙonawa.Da haka fa aka maido hidimar Haikalin Ubangiji.

36. Hezekiya da dukan jama'a suka yi murna saboda abin da Allah ya yi wa jama'a, gama farat ɗaya abin ya faru.

Karanta cikakken babi 2 Tar 29