Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 28:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. A wannan lokaci kuwa sarki Ahaz ya nemi taimako wurin sarakunan Assuriya.

17. Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su.

18. Filistiyawa kuma sun kai hari a biranen ƙasar Shefela, da Negeb ta Yahuza, har suka ci Bet-shemesh, da Ayalon, da Gederot, da Soko da ƙauyukanta, da Timna da ƙauyukanta, da Gimzo da ƙauyukanta. Sai suka zauna a can.

19. Ubangiji kuwa ya ƙasƙantar da Yahuza, saboda Ahaz Sarkin Yahuza ya yi ganganci a Yahuza, ya zama marar aminci ga Ubangiji.

20. Sai Tiglatfilesar, Sarkin Assuriya, ya zo ya yi yaƙi da shi, ya wahalshe shi, maimakon ya taimake shi.

21. Sai Ahaz ya kwaso kaya daga Haikalin Ubangiji, da fādar sarki, da na sarakuna, ya ba Sarkin Assuriya, amma sam, bai taimake shi ba.

22. Duk da wannan wahala da sarki Ahaz yake sha a wannan lokaci, sai ƙara rashin aminci yake yi ga Ubangiji.

23. Gama ya miƙa hadaya ga gumakan Dimashƙu, ga waɗanda suka ci shi da yaƙi, ya ce, “Saboda gumakan sarakunan Suriya sun taimake su, ni ma zan miƙa musu hadaya don su taimake ni.” Amma suka zama masa dalilin lalacewa, shi da dukan Isra'ila.

24. Sai Ahaz kuma ya tattara tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya farfashe su. Ya kuma kukkulle ƙofofin Haikalin Ubangiji, ya gina wa kansa bagadai a kowane lungu na Urushalima.

25. A kowane birni na Yahuza, ya yi masujadai inda zai ƙona turare ga gumaka, ya sa Ubangiji, Allah na kakanninsa ya yi fushi.

Karanta cikakken babi 2 Tar 28