Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 22:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya kuwa aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar gidan Ahab, gama su ne mashawartansa bayan rasuwar tsohonsa, wato shawarar da ta kai shi ga lalacewa.

5. Ya kuwa bi shawararsu. Ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab, Sarkin Isra'ila, don su yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya, a Ramot-gileyad. Suriyawa kuwa suka yi wa Yehoram rauni.

6. Don haka sai ya koma Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da aka yi masa a Rama, sa'ad da suka yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya ɗan Yoram, Sarkin Yahuza, ya gangara don ya gai da Yehoram ɗan Ahab a Yezreyel wanda yake rashin lafiya.

7. Allah ya ƙaddara hallakar Ahaziya ta zo ta wurin ziyarar da ya kai wa Yehoram. Gama sa'ad da ya zo, sai ya fita tare da Yehoram don su yi yaƙi da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya keɓe don ya kakkaɓe gidan Ahab.

8. Sa'ad da Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya gamu da sarakunan Yahuza, da 'ya'yan 'yan'uwan Ahaziya, maza, suna yi wa Ahaziya hidima, sai ya karkashe su.

9. Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.”Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.

10. Da Ataliya tsohuwar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta karkashe duk 'yan sarautar gidan Yahuza.

Karanta cikakken babi 2 Tar 22