Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 21:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Yoram yana da shekara talatin da biyu sa'ad da ya hau gadon sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara takwas.

6. Ya yi yadda sarakunan Isra'ila suka yi, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama matarsa 'yar Ahab ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

7. Duk da haka Ubangiji bai yarda ya hallaka gidan Dawuda ba, saboda alkawarin da ya riga ya yi da Dawuda, gama ya riga ya alkawarta zai ba shi haske, shi da 'ya'yansa maza har abada.

8. A zamaninsa Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.

9. Sai Yoram ya wuce, shi da shugabannin sojojinsa tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare ya fatattaki Edomawa waɗanda suka kewaye shi, shi da shugabannin karusansa.

10. Har wa yau Edom ya tayar wa Yahuza. A wannan lokaci kuma Libna ta tayar wa mulkinsa, saboda Yoram ya rabu da bin Ubangiji Allah na kakanninsa.

11. A kan wannan kuma, ya yi masujadai a tuddan ƙasar Yahuza, ya sa mutanen Urushalima su zama marasa aminci, ya sa Yahuza ta ratse.

12. Sai annabi Iliya ya rubuta masa wasiƙa ya ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na tsohonka Dawuda ya ce, ‘Da yake ba ka bi halin tsohonka Yehoshafat ba, da halin Asa Sarkin Yahuza,

Karanta cikakken babi 2 Tar 21