Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Tar 2:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra'ila.

5. Haikalin nan kuwa da nake niyyar ginawa babba ne, gama Allahnmu ya fi dukan alloli.

6. Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa?

7. Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.

8. Ka kuma aiko mini da itacen al'ul, da na fir, da katakon algum daga Lebanon, gama na sani barorinka sun san yadda ake yanyanka katakan Lebanon. Barorina za su yi aiki tare da barorinka,

9. domin su shirya mini katako mai yawa. Gama Haikalin da zan gina mai girma ne ƙwarai, mai banmamaki.

10. Zan ba barorinka masu aikin katako misalin mudu dubu ashirin (20,000) ta sussukakkiyar alkama, da mudu dubu ashirin (20,000) ta sha'ir, da misalin garwar ruwan inabi dubu ashirin (20,000), da ta mai dubu ashirin (20,000).”

11. Hiram, Sarkin Taya kuwa, ya ba Sulemanu amsar takardarsa, ya ce, “Saboda Ubangiji yana ƙaunar jama'arsa, ya naɗa ka sarkinsu.”

12. Hiram ya ci gaba da cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya yi sama da ƙasa, ya ba sarki Dawuda ɗa mai hikima, mai hankali, mai ganewa, wanda zai gina Haikali dominsa, ya gina fāda kuma domin kansa.

Karanta cikakken babi 2 Tar 2