Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 9:19-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ya kuma aiki wani, na biyu, a kan doki, ya je wurinsu ya ce musu, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”Yehu ya amsa, ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”

20. Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”

21. Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa'an nan Yehoram Sarkin Isra'ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel.”

22. Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?”Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?

23. Yehoram kuwa ya juyar da karusarsa baya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Maƙarƙashiya ce, ya Ahaziya!”

24. Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa.

25. Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa'ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa,

26. ‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”

27. Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.

28. Fādawansa suka ɗauke shi a cikin karusar zuwa Urushalima, suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

29. Ahaziya ya ci sarautar Yahuza a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Yehoram ɗan Ahab.

30. Da Yezebel ta ji Yehu ya zo Yezreyel, sai ta shafa wa idanunta launi, ta gyara gashin kanta, sa'an nan ta leƙa ta taga.

31. Da Yehu ya shiga ƙofar garin, sai ta ce, “Kai Zimri, mai kashe maigidansa, me kake yi a nan?”

32. Sai ya ɗaga idanunsa wajen tagar, ya ce, “Wa yake wajena?” Sai babani biyu ko uku suka dube shi,

33. shi kuwa ya ce, “Ku wurgo ta ƙasa.” Sai suka wurgo ta ƙasa. Jininta ya fantsama a jikin bangon da jikin dawakan da suka tattake ta.

34. Sa'an nan Yehu ya shiga gida, ya ci ya sha, ya ce, “Ku san yadda za ku yi da wannan la'ananniyar mace, ku binne ta, gama ita 'yar sarki ce.”

35. Amma da suka tafi don su binne ta, ba su tarar da kome ba sai ƙwaƙwalwa, da ƙafafu, da tafin hannuwanta.

36. Sai suka komo, suka faɗa masa. Sai ya ce musu, “Wannan, ai, faɗar Ubangiji, wadda ya faɗa ta bakin bawansa Iliya Batishbe, ya ce, ‘Karnuka za su cinye naman Yezebel a cikin Yezreyel.

Karanta cikakken babi 2 Sar 9