Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 8:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ya bi halin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama ya auri 'yar Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji.

19. Duk da haka Ubangiji bai hallaka Yahuza ba, saboda bawansa Dawuda, tun da yake ya alkawarta zai ba shi haske, shi da 'ya'yansa har abada.

20. A zamanin Yoram, Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.

21. Sa'an nan Yoram ya haye zuwa Zayar tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare da shugabannin karusansa, ya bugi Edomawan da suka kewaye shi, amma sojojinsa suka gudu zuwa alfarwansu.

22. Haka kuwa Edom ta tayar wa Yahuza har wa yau. A lokacin kuma Libna ta tayar wa Yahuza.

23. Sauran ayyukan Yoram da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

24. Yoram kuwa ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Ahaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.

25. A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Yehoram ɗan Ahab Sarkin Isra'ila, Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

26. Ya ci sarauta yana da shekara ashirin da biyu da haihuwa, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikanyar Omri, Sarkin Isra'ila.

27. Ya ɗauki halin gidan Ahab. Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama shi surukin gidan Ahab ne.

28. Sarki Ahaziya kuwa ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab don su yi yaƙi da Hazayel, Sarkin Suriya, a Ramot cikin Gileyad. Suriyawa suka yi wa Yehoram rauni.

29. Sai sarki Yehoram ya koma zuwa Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da yake yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya, ɗan Yoram, Sarkin Yahuza ya tafi ya ziyarci Yehoram ɗan Ahab cikin Yezreyel saboda yana ciwo.

Karanta cikakken babi 2 Sar 8