Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 7:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma Elisha ya ce, “Kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce! Gobe war haka za a sayar da mudu na lallausan gari a bakin shekel guda, da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel guda a ƙofar garin Samariya.”

2. Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.”Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”

3. Akwai mutum huɗu, kutare, waɗanda suke zaune a bakin ƙofar gari, sai suka ce wa junansu, “Me ya sa muke zaune nan har mu mutu?

4. Idan mun ce, ‘Bari mu shiga birni,’ yunwa tana birnin, za mu mutu a wurin. Idan kuma mun zauna a nan za mu mutu. Saboda haka bari mu tafi sansanin Suriyawa, idan sun bar mu da rai, za mu rayu, idan kuwa sun kashe mu, za mu mutu.”

5. Sai suka tashi da magariba, suka tafi sansanin Suriyawa. Da suka isa gefen sansanin Suriyawa, sai suka tarar ba kowa a wurin,

6. gama Ubangiji ya sa sojojin Suriyawa suka ji amon karusai, da na dawakai, da na babbar rundunar soja. Sai suka ce wa junansu, “Ai, Sarkin Isra'ila, ya yi ijara da sarakunan Hittiyawa, da na Masarawa, su zo su fāɗa mana.”

7. Saboda haka suka gudu da almuru, suka bar alfarwansu, da dawakansu, da jakunansu, suka bar sansanin yadda yake, suka tsira da rayukansu.

8. Sa'ad da kutaren nan suka zo sansanin, sai suka shiga wata alfarwa, suka ci suka sha. Suka kwashe azurfa, da zinariya, da tufafi, suka tafi suka ɓoye. Suka koma suka shiga wata alfarwa kuma, suka kwashe abubuwan da suke cikinta. Suka tafi suka ɓoye su.

9. Sa'an nan suka ce wa junansu, “Ba mu kyauta ba. Yau ranar albishir ce, idan mun yi shiru, mun jira har safe, wani mugun abu zai same mu. Domin haka bari mu tafi mu faɗa a gidan sarki.”

10. Sai suka tafi wurin masu gadin ƙofar birnin, suka ce musu, “Mun tafi sansanin Suriyawa ba mu ga kowa ba, ba mu kuma ji motsin kowa a wurin ba, ba kowa a wurin sai dawakai da jakai, a ɗaure, alfarwai kuma suna nan yadda suke.”

Karanta cikakken babi 2 Sar 7