Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 3:5-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Amma da Ahab ya rasu, Sarkin Mowab kuwa ya tayar wa Sarkin Isra'ila.

6. Sai sarki Yehoram ya fita daga Samariya a lokacin, ya tattara Isra'ila duka.

7. Ya kuma aika wa Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ce, “Sarkin Mowab ya tayar mini, ko za ka yarda ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowabawa?”Yehoshafat ya ce, “Zan tafi, ni kamarka ne, mutanena kuma kamar mutanenka, dawakaina kuma kamar naka.

8. Wace hanya za mu bi?”Yehoram kuwa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”

9. Yehoram Sarkin Isra'ila ya tafi tare da Sarkin Yahuza da Sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

10. Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya ce, “Kaito! Ubangiji ya kirawo mu sarakunan nan uku don ya bashe mu a hannun Mowabawa.”

11. Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji ne a nan, wanda zai tambayar mana Ubangiji?”Sai ɗaya daga cikin fādawan Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, na'ibin Iliya.”

12. Yehoshafat kuwa ya ce, “Gaskiya ne, maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sai sarakunan nan uku suka ɗunguma zuwa wurin Elisha.

13. Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.”Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”

14. Elisha ya amsa ya ce, “Na rantse da Ubangiji Mai Runduna, wanda nake bautarsa, da ba domin ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuza ba, da ba zan kula da kai har ma in dube ka ba.

15. Amma yanzu ku kawo mini makaɗin garaya.”Da makaɗin garaya ya kaɗa, sai ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha.

Karanta cikakken babi 2 Sar 3