Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 19:5-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'ad da fādawan sarki Hezekiya suka iso wurin Ishaya,

6. sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, ‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni.

7. Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”

8. Rabshake kuwa ya koma, ya tarar Sarkin Assuriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji labari sarki ya riga ya bar Lakish.

9. Da sarki ya ji labari Tirhaka, Sarkin Habasha, ya fito don ya yi yaƙi da shi, sai ya sāke aikar manzanni wurin Hezekiya, ya ce,

10. “Ku faɗa wa Hezekiya Sarkin Yahuza, kada ya yarda Allahnsa wanda yake dogara gare shi ya yaudare shi da yi masa alkawari, cewa Sarkin Assuriya ba zai ci Urushalima ba.

11. Ya ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa dukan ƙasashe yadda ya hallaka su sarai. To, shi zai kuɓuta?

12. Allolin al'ummai sun cece su ne? Wato al'umman da kakannina suka hallaka, wato Gozan, da Haran, da Rezef, da mutanen Eden da suke Telassar.

13. Ina Sarkin Hamat, da Sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarwayim, da Sarkin Hena, da Sarkin Iwwa?”

14. Hezekiya ya karɓi wasiƙa daga hannun manzannin ya karanta ta, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji, ya buɗe ta, ya ajiye ta a gaban Ubangiji.

15. Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.

16. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka yi. Ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka gani, ka kuma ji irin maganar Sennakerib wadda ya aiko don a yi wa Allah mai rai ba'a.

17. A gaskiya kam, ya Ubangiji, sarakunan Assuriya sun lalatar da al'ummai da ƙasashensu.

18. Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su.

19. Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”

20. Sa'an nan Ishaya, ɗan Amoz, ya aika wa Hezekiya cewa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ji addu'arka, ya kuma amsa.”

21. Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba'a.

22. Wa kake tsammani ka yi wa ba'a har da zagi? Ba ka ga girmana ba, ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila?

23. Ka aiki manzanninka su nuna mini girmankai saboda ka ci duwatsu mafi tsayi da karusanka, har ma ka ci duwatsun Lebanon. Ka yi fariyar a kan ka datse itatuwan al'ul mafi tsayi da na fir, har kuma ka shiga har can tsakiyar kurmi.

Karanta cikakken babi 2 Sar 19