Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 19:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”

20. Sa'an nan Ishaya, ɗan Amoz, ya aika wa Hezekiya cewa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ji addu'arka, ya kuma amsa.”

21. Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba'a.

22. Wa kake tsammani ka yi wa ba'a har da zagi? Ba ka ga girmana ba, ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila?

23. Ka aiki manzanninka su nuna mini girmankai saboda ka ci duwatsu mafi tsayi da karusanka, har ma ka ci duwatsun Lebanon. Ka yi fariyar a kan ka datse itatuwan al'ul mafi tsayi da na fir, har kuma ka shiga har can tsakiyar kurmi.

24. Ka yi fariya a kan gina rijiyoyi, ka sha ruwan baƙuwar ƙasa, ƙafafun sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu, ya ƙafe.

25. “Ba ka taɓa ji ba, cewa na ƙaddara wannan tun dā? Abin da yake faruwa yanzu, na shirya shi tun tuni, yadda za ka mai da birane masu garu su zama kufai.

26. Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.

27. “Na san zamanka, da fitarka, da shigowarka, da fushin da kake yi da ni.

28. Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”

29. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci 'ya'yansu.

Karanta cikakken babi 2 Sar 19