Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 17:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Ahaz Samariya Yahuza, Hosheya ɗan Ila ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara tara.

2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar sauran sarakunan Isra'ila da suka riga shi ba.

3. Sai Shalmanesar Sarkin Assuriya, ya kawo masa yaƙi, Hosheya kuwa ya zama talakansa, yana kai masa haraji.

4. Amma Sarkin Assuriya ya gane Hosheya ya tayar masa, gama ya aiki manzanni wurin So, wato Sarkin Masar, ya kuma ƙi ya kai wa Sarkin Assuriya haraji kamar yadda ya saba yi kowace shekara, Saboda haka sai Sarkin Assuriya ya kama shi ya sa shi a kurkuku.

5. Sa'an nan Sarkin Assuriya ya kai wa dukan ƙasar yaƙi, har ya kai Samariya. Ya kewaye Samariya da yaƙi shekara uku.

6. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.

7. Wannan abu ya sami Isra'ila saboda sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fito da su daga ƙasar Masar, daga hannun Fir'auna, Sarkin Masar. Suka bauta wa gumaka.

8. Suka bi al'adun al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora a gabansu, da al'adun da sarakunan Isra'ila suka kawo.

9. Jama'ar Isra'ila kuma suka yi wa Ubangiji Allahnsu abubuwan da ba daidai ba, daga ɓoye. Sun gina wa kansu matsafai a dukan garuruwansu daga hasumiya zuwa birni mai garu.

10. Suka kuma kafa wa kansu ginshiƙai da siffofin gumakan Ashtarot a kowane tudu da a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.

11. Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.

Karanta cikakken babi 2 Sar 17