Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 16:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

2. Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarautar, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Bai yi abin da yake da kyau a gaban Ubangiji Allahnsa ba, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.

3. Ya bi halin sarakunan Isra'ila. Har ma ya yi hadaya ta ƙonawa da ɗansa, kamar mugayen ayyukan al'ummai da Ubangiji ya kora a gaban mutanen Isra'ila.

4. Ya kuma miƙa hadaya da turaren ƙonawa a wuraren tsafi na kan tuddai da ƙarƙashin itatuwa masu duhuwa.

5. Rezin Sarkin Suriya kuwa, da Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, suka kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye Ahaz da yaƙi, amma ba su ci shi ba.

6. A lokacin nan kuma Sarkin Edom ya sāke ƙwace Elat, ya kori Yahudawa daga cikinta, Edomawa suka zo suka zauna a ciki har wa yau.

7. Ahaz kuwa ya aiki manzanni wurin Tiglat-filesar, mai mulkin Assuriya, ya ce, “Ni baranka ne, ɗanka kuma, ka zo ka cece ni daga hannun Sarkin Suriya da Sarkin Isra'ila, waɗanda suke yaƙi da ni.”

8. Ahaz kuma ya kwashe azurfa da zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, da wadda take cikin baitulmalin sarki, ya aika wa mai mulkin Assuriya kyauta.

9. Tiglat-filesar ya ji roƙonsa, sai ya zo ya faɗa wa Dimashƙu da yaƙi, ya ci ta. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa Kir. Ya kuma kashe sarki Rezin.

10. Sa'ad da sarki Ahaz ya tafi Dimashƙu don ya sadu da Tiglat-filesar, Sarkin Assuriya, ya ga bagaden da yake a Dimashƙu, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayaninsa.

11. Uriya firist kuwa, ya gina bagaden bisa ga yadda sarki Ahaz ya aika masa daga Dimashƙu. Uriya firist, ya gina bagaden kafin sarki Ahaz ya komo daga Dimashƙu.

12. Da sarki ya komo daga Dimashƙu, ya hango bagaden, sai ya tafi kusa da shi.

13. Sa'an nan ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayarsa ta gari, da hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta salama a bisa bagaden.

Karanta cikakken babi 2 Sar 16