Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 14:9-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Yehowash Sarkin Isra'ila ya mayar wa Amaziya Sarkin Yahuza da amsa cewa, “A dutsen Lebanon ƙaya ta aika wurin itacen al'ul ta ce, ‘Ka ba ɗana 'yarka ya aura.’ Sai mugun naman jeji na Lebanon ya wuce, ya tattake ƙayar.

10. Yanzu kai, Amaziya, ka bugi Edomawa don haka zuciyarka ta kumbura. To ka gode da darajar da ka samu, ka tsaya a gida, gama don me kake tonon rikici da zai jawo maka fāduwa, kai da mutanen Yahuza?”

11. Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza a Bet-shemesh ta Yahuza.

12. Mutanen Isra'ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida.

13. Yehowash Sarkin Isra'ila kuwa ya kama Amaziya, Sarkin Yahuza, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-shemesh. Ya kuma zo Urushalima ya rushe garun Urushalima kamu ɗari huɗu daga Ƙofar Ifraimu zuwa Ƙofar Kusurwa.

14. Ya kwashe dukan zinariya, da azurfa, da dukan kwanonin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na baitulmalin gidan sarki, da mutanen da aka ba da su jingina, sa'an nan ya koma Samariya.

15. Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yadda ya yi yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

16. Yehowash ya mutu, aka binne shi a Samariya a makabartar sarakunan Isra'ila, Ɗansa Yerobowam na biyu ya gāji sarautarsa.

17. Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila.

18. Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

19. Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can.

20. Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda.

21. Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya.

22. Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.

23. A shekara goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash Sarkin Isra'ila, ya ci sarauta a Samariya. Ya yi mulki shekara arba'in da ɗaya.

24. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.

Karanta cikakken babi 2 Sar 14