Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 13:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”

15. Elisha kuwa ya ce masa, “Ka ɗauki baka da kibau.” Shi kuwa ya ɗauka.

16-17. Sa'an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa'an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”

18. Sa'an nan ya ce, “Ka ɗauki kibau.” Shi kuwa ya ɗauka. Sai ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka caki ƙasa da su.” Sai ya caka har sau uku, sa'an nan ya tsaya.

19. Elisha kuwa ya husata, ya ce, “Da ma ka caka sau biyar ko shida da za ka yi nasara a kan Suriyawa har ka ci su sarai, amma yanzu za ka yi nasara da su sau uku kawai.”

20. Elisha kuwa ya rasu, aka binne shi.Maharan Mowabawa sukan kawo yaƙi a ƙasar da bazara.

21. Wata rana ana binne gawa, sai aka ga mahara, aka jefar da gawar a cikin kabarin Elisha. Da gawar ta taɓi ƙasusuwan Elisha, sai ya farko ya tashi ya miƙe tsaye.

22. Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya musguna wa jama'ar Isra'ila a dukan zamanin Yehowahaz.

23. Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.

24. Da Hazayel Sarkin Suriya ya rasu, sai Ben-hadad ɗansa ya gāji sarautarsa.

25. Sai Yehowash ɗan Yehowahaz ya ƙwace daga hannun Ben-hadad, ɗan Hazayel, biranen da Ben-hadad ya ci da yaƙi daga hannun Yehowahaz, tsohonsa. Sau uku Yehowash ya ci shi da yaƙi, sa'an nan ya karɓe biranen Isra'ila.

Karanta cikakken babi 2 Sar 13