Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 21:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sarki kuwa ya bai wa Gibeyonawa su. Sai suka rataye su a kan dutse a gaban Ubangiji. Su bakwai ɗin nan suka hallaka gaba ɗaya. An kashe su a farkon kakar sha'ir.

10. Rizfa kuwa, 'yar Aiya, ta ɗauki algarara ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutsen. Ta zauna a wurin tun daga farkon kaka har zubar ruwan damuna da ya bugi gawawwakin. Ba ta bar tsuntsaye su sauka a kansu da rana ba, ko namomin jeji da dare.

11. Sa'ad da aka sanar wa Dawuda abin da Rizfa, 'yar Aiya, ƙwarƙwarar Saul ta yi,

12. Dawuda ya tafi ya kwaso ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan daga wurin mutanen Yabesh a Gileyad. (Gama suka sace su daga dandalin Bet-sheyan, a inda Filistiyawa suka rataye su, a ranar da suka kashe Saul a Gilbowa.)

13. Daga can ne ya kwaso ƙasusuwan Saul da na Jonatan, suka kuma tattara ƙasusuwan waɗanda aka rataye.

14. Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu'arsu a kan ƙasar.

15. Ana nan sai Filistiyawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi. Dawuda kuwa ya gangara tare da jama'arsa, suka yi yaƙi da Filistiyawa. Dawuda kuwa ya gaji.

16. Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda.

Karanta cikakken babi 2 Sam 21