Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 20:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sa'an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mini mutanen Yahuza kafin kwana uku, kai kuma ka zo tare da su.”

5. Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuza, amma ya makara, bai zo a lokacin da aka ƙayyade masa ba.

6. Dawuda kuma ya ce wa Abishai, “Sheba ɗan Bikri fa, zai ba mu wuya fiye da Absalom, sai ka ɗauki mutanena, ka bi sawunsa, don kada ya ci garuruwa masu garu har ya tsere mana.”

7. Sa'an nan mutanen Yowab, wato Keretiyawa da Feletiyawa, da dukan jarumawa, suka bi bayan Abishai. Suka fita daga Urushalima don su bi sawun Sheba, ɗan Bikri.

8. Sa'ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi.

9. Yowab ya ce wa Amasa, “Abokina kana lafiya?” Yowab kuma ya kama gemun Amasa da hannun dama don ya sumbace shi.

10. Amma Amasa bai lura Yowab yana da takobi a hannunsa ba. Yowab kuwa ya kirɓa masa takobin a ciki sau ɗaya, sai hanjin Amasa ya zuba ƙasa, ya mutu.Sa'an nan Yowab da Abishai ɗan'uwansa suka bi sawun Sheba, ɗan Bikri.

11. Sai ɗaya daga cikin samarin Yowab ya tsaya kusa da gawar Amasa ya ce, “Duk wanda yake son Yowab da duk wanda yake goyon bayan Dawuda, ya bi Yowab.”

12. Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya.

13. Sa'ad da aka kawar da ita daga kan hanya, dukan mutane kuwa suka bi Yowab domin su bi sawun Sheba ɗan Bikri.

Karanta cikakken babi 2 Sam 20