Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 19:29-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Sai sarki ya ce masa, “Me ya kawo wannan magana a kan harkokinka? Ai, na riga na zartar, cewa, kai da Ziba za ku raba mallakar Saul.”

30. Mefiboshet ya ce wa sarki, “A ma bar masa duka ya mallaka, ni dai tun da ubangijina, sarki, ya komo gida lafiya, to, alhamdu lillahi.”

31. Barzillai Bagileyade kuma ya gangara daga Rogelim zuwa wurin sarki domin ya yi wa sarki rakiya zuwa hayin Urdun.

32. Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa'ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne.

33. Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka zo mu tafi tare zuwa Urushalima, ni kuwa zan riĆ™a biya maka bukata.”

34. Amma Barzillai ya amsa, ya ce, “Shekaruna nawa suka ragu har da zan tafi Urushalima tare da sarki?

Karanta cikakken babi 2 Sam 19