Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 19:27-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Barana ya ɓata sunana a gaban ubangijina, sarki. Amma ranka ya daɗe, ya sarki, kai kamar mala'ikan Allah kake, sai ka yi abin da ya yi maka daidai.

28. Gama dukan mutanen gidan kakana sun cancanci mutuwa a gabanka, ranka ya daɗe, amma ga shi, ka sa na zama ɗaya daga cikin waɗanda suke ci a teburinka. Ba ni da dalilin da zai sa in yi wa sarki wani kuka kuma.”

29. Sai sarki ya ce masa, “Me ya kawo wannan magana a kan harkokinka? Ai, na riga na zartar, cewa, kai da Ziba za ku raba mallakar Saul.”

30. Mefiboshet ya ce wa sarki, “A ma bar masa duka ya mallaka, ni dai tun da ubangijina, sarki, ya komo gida lafiya, to, alhamdu lillahi.”

31. Barzillai Bagileyade kuma ya gangara daga Rogelim zuwa wurin sarki domin ya yi wa sarki rakiya zuwa hayin Urdun.

32. Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa'ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne.

33. Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka zo mu tafi tare zuwa Urushalima, ni kuwa zan riƙa biya maka bukata.”

34. Amma Barzillai ya amsa, ya ce, “Shekaruna nawa suka ragu har da zan tafi Urushalima tare da sarki?

35. A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe.

36. Ban cancanci wannan irin babban lada ba. Zan dai yi maka 'yar rakiya zuwa hayin Urdun.

37. Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”

38. Sarki ya ce, “To, Kimham zai tafi tare da ni, zan kuwa yi masa abin da zai yi maka daɗi. Duk abin da kake so a gare ni, zan yi maka.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 19