Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 15:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Sa'an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa.

26. Amma idan Ubangiji bai ji daɗina ba, to, ga ni, sai ya yi yadda ya ga dama da ni.”

27. Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.

28. Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”

29. Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.

30. Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa'ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka.

31. Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.”Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”

32. Da Dawuda ya hau kan dutse inda ake yi wa Allah sujada, sai ga amininsa Hushai Ba'arkite, da ketacciyar riga, da ƙura a kansa, ya zo ya taryi Dawuda.

33. Dawuda kuwa ya ce masa, “Idan ka tafi tare da ni za ka zama mini nawaya.

34. Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, ‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.’ Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.

35. Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci.

36. Ga 'ya'yansu biyu suna tare da su a can, wato Ahimawaz, ɗan Zadok, da Jonatan, ɗan Abiyata. Duk abin da ka ji, ka aiko su, su zo su faɗa mini.”

37. Hushai, abokin Dawuda kuwa, ya isa Urushalima daidai lokacin da Absalom yake shiga.

Karanta cikakken babi 2 Sam 15