Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 13:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Absalom, ɗan Dawuda, yana da kyakkyawar ƙanwa, sunanta Tamar. Ana nan Amnon ɗaya daga cikin 'ya'yan Dawuda, ya ƙaunace ta.

2. Amnon ya matsu har ya fara ciwo saboda Tamar ƙanwarsa. Ita kuwa budurwa ce, ba shi yiwuwa Amnon ya yi wani abu da ita.

3. Amma Amnon yana abuta da Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda. Yonadab kuwa yana da hila.

4. Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?”Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan'uwana Absalom.”

5. Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, ‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.’ ”

6. Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo.Sa'ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”

7. Sai Dawuda ya aika gida, wurin Tamar, ya ce, “Tafi gidan Amnon wanki, ki shirya masa abinci.”

8. Tamar kuwa ta tafi gidan wanta Amnon, inda yake kwance. Sai ta ɗauki ƙullu, ta cuɗa, ta toya waina a idonsa.

9. Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.

10. Sa'an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.

11. Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 13