Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 12:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra'ila, na cece ka daga hannun Saul.

8. Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra'ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.

9. Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.

10. Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.

11. Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā.

12. Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra'ila da rana katā.’ ”

13. Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.

14. Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”

15. Sa'an nan Natan ya tafi gida.Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.

16. Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.

17. Sai fādawansa suka zo suka kewaye shi, don su tashe shi daga ƙasa, amma bai yarda ba, bai kuma ci abinci tare da su ba.

Karanta cikakken babi 2 Sam 12