Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 12:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.

2. Basaraken yana da garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu.

3. Amma talakan ba shi da kome sai 'yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da 'ya'yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar 'ya a gare shi.

4. Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo 'yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”

5. Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa.

6. Sai kuma ya biya diyyar 'yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”

7. Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra'ila, na cece ka daga hannun Saul.

Karanta cikakken babi 2 Sam 12