Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 9:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. 'Yan'uwansu waɗanda suke a ƙauyuka kuwa, ya zamar musu wajibi su zo wurinsu kowane kwana bakwai, domin su karɓe su tsaron.

26. Su shugabanni huɗu na matsaran ƙofar Lawiyawa ne waɗanda suke da matsayi na riƙon amana, su ne masu lura da ɗakunan Haikalin Allah da dukiyarsa.

27. Sukan kwana suna tsaro kewaye da Haikalin Allah, gama hakkin yana kansu. Su ne sukan buɗe shi kowace safiya.

28. Waɗansunsu suna lura da kayayyakin aiki na cikin Haikali. Sukan ƙidaya su sa'ad da aka shigo da su, da sa'ad da aka fitar da su.

29. Aka sa waɗansu su zama masu lura da kayayyakin Haikalin, da kayayyakin aiki na cikin Wuri Mai Tsarki, da lallausan gari, da ruwan inabi, da mai, da turare, da kayan yaji.

30. Waɗansu 'ya'yan firistoci, maza, suke harhaɗa kayan yaji.

31. Mattitiya, ɗaya daga cikin Lawiyawa, ɗan farin Shallum na iyalin Kora, shi ne mai lura da toya waina.

32. Waɗansu 'yan'uwansu Kohatawa suke lura da gurasar ajiyewa. Sukan shirya ta kowace Asabar.

33. Waɗannan su ne mawaƙa, da shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa, waɗanda suka zauna a ɗakunan Haikali, ba su yin wani aiki dabam, gama dare da rana suke yin aikinsu.

34. Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa a zamaninsu, wato waɗanda suka zauna a Urushalima.

35. Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma'aka,

36. ɗan farinsa kuma shi ne Abdon. Sa'an nan ga Zur, da Kish, da Ba'al, da Ner, da Nadab,

37. da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, da Miklot,

Karanta cikakken babi 1 Tar 9