Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 9:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. da kuma Bakbakkar, da Heresh, da Galal, da Mattaniya ɗan Mika wanda kakanninsa su ne Zikri da Asaf,

16. da kuma Obadiya ɗan Shemaiya, kakanninsa su ne Galal da Yedutun, da Berikiya ɗan Asa, wato jīkan Elkana, wanda ya zauna a garin Netofa.

17. Masu tsaron Haikalin, su ne Shallum, da Akkub, da Talmon, da Ahiman, da 'yan'uwansu. Shallum shi ne shugaba.

18. Har zuwa yau, iyalinsu suke tsaron ƙofar sarki a wajen gabas. A dā su ne suke tsaron sauran ƙofofin zangon Lawiyawa.

19. Shallum ɗan Kore, wato jīkan Ebiyasaf, tare da 'yan'uwansa na zuriyar Kora, suke lura da masu tsaron ƙofofin alfarwa kamar dai yadda kakanninsu suka lura da zangon Ubangiji.

20. A dā Finehas ɗan Ele'azara shi ne shugabansu, Ubangiji kuwa yana tare da shi.

21. Zakariya ɗan Shallum yake tsaron ƙofar alfarwa ta sujada.

22. Dukan waɗanda aka zaɓa domin su zama masu tsaron ƙofofi, su ɗari biyu ne da goma sha biyu. An lasafta su bisa ga asalinsu da garuruwansu. Dawuda da Sama'ila annabi, su ne suka sa su a matsayinsu na riƙon amana.

23. Saboda haka su da 'ya'yansu maza suke tsaron ƙofofin Ubangiji, wato alfarwa ta sujada.

24. Matsaran ƙofofi suka tsaya a kusurwoyi huɗu, wato gabas da yamma, kudu da arewa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 9