Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 4:10-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.

11. Kalibu ɗan'uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.

12. Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.

13. 'Ya'yan Kenaz, maza, su ne Otniyel da Seraiya. Yana kuma da waɗansu 'ya'ya maza, su ne Hatata da Meyonotai.

14. Meyonotai kuwa shi ne mahaifin Ofra.Seraiya shi ne ya haifi Yowab, Yowab ya kafa kwarin Ge-harashim, saboda su masu sana'a ne.

15. 'Ya'yan Kalibu, maza, ɗan Yefunne, su ne Airu, da Ila, da Na'am. Ila shi ya haifi Kenaz.

16. 'Ya'yan Yehallelel, maza, su ne Zif, da Zifa, da Tiriya, da Asarel.

17-18. 'Ya'yan Ezra, maza, su ne Yeter, da Mered, da Efer, da Yalon. Bitiya 'yar Fir'auna, wadda Mered ya aura, ta haifi waɗannan, Maryamu, da Shammai, da Ishaba wanda ya haifi Eshtemowa. Mered kuma ya auri wata daga kabilar Yahuza, ta haifi Yered wanda ya kafa garin Gedor. Eber kuma ya kafa garin Soko, Yekutiyel kuwa ya kafa garin Zanowa.

19. 'Ya'ya maza na matar Hodiya 'yar'uwar Naham, su ne suka zama kakannin Kaila, Bagarme, da Eshtemowa da suke zaune a Ma'aka.

20. 'Ya'yan Shimon, maza, su ne Amnon, da Rinna, da Ben-hanan, da Tilon.'Ya'yan Ishi, maza kuwa, su ne Zohet da Ben-zohet.

21. 'Ya'yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La'ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,

22. da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa'an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)

23. Su ne maginan tukwane, waɗanda suke zaune a Netayim da Gedera. Sun zauna tare da sarki don su yi masa aiki.

24. 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, da Zohar, da Shawul,

25. da Shallum ɗansa, da Mibsam jīkansa, da Mishma jīkan ɗansa.

26. 'Ya'yan Mishma, maza, su ne Hammuwel, da Zakkur, da Shimai.

Karanta cikakken babi 1 Tar 4