Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 28:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.

10. Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”

11. Sa'an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.

12. Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.

13. Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji.

14. Ya kuma faɗa wa Sulemanu yawan zinariya da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita don yin aiki,

15. da yawan zinariya da za a yi alkukan fitilu, da kuma fitilun, da yawan zinariya da za a yi kowane alkuki da fitilunsa, da yawan azurfa da za a yi alkuki bisa ga yadda za a yi amfani da kowane alkuki,

16. da yawan zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa, da azurfar da za a yi teburorin azurfa,

17. da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsotsi, da daruna, da finjalai, da kwanoni da ita, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita,

18. da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita. Ya kuma ba shi tsarin zinariya ta kerubobin da za su miƙe fikafikansu su rufe akwatin alkawari na Ubangiji.

19. Sarki Dawuda ya ce, “Dukan wannan rubutacce ne daga wurin Ubangiji zuwa gare ni domin in fahimci fasalin aikin filla filla.”

20. Sarki Dawuda kuma ya ce wa ɗansa Sulemanu, “Ka yi ƙarfin hali, ka dāge sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji Allah, wato Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ba, ba kuwa zai rabu da kai ba, har ka gama dukan aikin Haikalin.

21. Ga dai ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, suna nan domin yin hidima a Haikalin Allah, ga kuma gwanaye na kowace irin sana'a suna tare da kai don yin kowane irin aiki. Shugabanni da dukan jama'a suna ƙarƙashinka duka.”

Karanta cikakken babi 1 Tar 28