Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 26:24-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami'in baitulmalin.

25. Ta wurin ɗan'uwan Gershom, wato Eliyezer ya sami dangantaka da Shelomit. Eliyezer shi ne mahaifin Rehabiya, wanda ya haifi Yeshaya, uban Yoram, da Zikri, da Shelomit.

26. Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.

27. Daga cikin ganimar yaƙi suka keɓe wani sashi domin gyaran Haikalin Ubangiji.

28. Dukan kuma abin da Sama'ila annabi, da Saul ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruya, suka keɓe an sa su a hannun Shelomit da 'yan'uwansa.

29. Kenaniya da 'ya'yansa maza na wajen Izhara su ne aka danƙa wa al'amuran sasantawa na Isra'ilawa, wato sun zama shugabanni da alƙalai.

30. Hashabiya da 'yan'uwansu, su dubu da ɗari bakwai (1,700), gwanaye ne, daga zuriyar Hebron, su ne suke lura da Isra'ilawan yamma da Urdun a kan aikin Ubangiji da na sarki.

31. Yeriya shi ne shugaban zuriyar Hebron bisa ga asalinsu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dawuda, sai aka bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a cikinsu, a Yazar ta Gileyad.

32. Sarki Dawuda ya sa shi, shi da 'yan'uwansu su dubu biyu da ɗari bakwai (2,700) gwanaye, waɗanda suke shugabancin gidajen kakanni, su lura da kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da rabin kabilar Manassa a kan dukan ayyukan Allah da na sarki.

Karanta cikakken babi 1 Tar 26