Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 23:23-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. 'Ya'yan Mushi, maza, su uku ne, wato Mali, da Eder, da Yerimot.

24. Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga gidajen kakanninsu, wato su ne shugabannin da aka rubuta sunayensu ɗaya ɗaya daga mai shekara ashirin da haihuwa zuwa sama. Su ne za su yi hidima a cikin Haikalin Ubangiji.

25. Gama Dawuda ya ce, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya hutar da jama'arsa, yana kuwa zama a Urushalima har abada.

26. Yanzu Lawiyawa ba za su riƙa ɗaukar alfarwar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta ba.”

27. Bisa ga maganar Dawuda ta ƙarshe aka ƙidaya 'ya'yan Lawiyawa, maza, daga mai shekara ashirin zuwa sama.

28. Aikinsu shi ne su taimaki 'ya'yan Haruna, maza, gudanar da aiki cikin Haikalin Ubangiji, wato lura da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan abubuwa, da yin taimako cikin kowace hidimar Haikalin Ubangiji.

29. Za su kuma taimaka wajen gurasar ajiyewa, da lallausan gari na hadaya ta gari, da waina marar yisti, da abin da akan toya, da abin da akan kwaɓa, da ma'aunan nauyi da na girma.

30. Za su kuma riƙa tsayawa kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Haka kuma za su riƙa yi da maraice,

31. da kuma lokacin miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa a ranakun Asabar, da lokacin tsayawar amaryar wata, da lokacin ƙayyadaddun idodi, za su tsaya a gaban Ubangiji bisa ga yawansu da ake bukata.

32. Su ne za su riƙa lura da alfarwa ta sujada, da Wuri Mai Tsarki, za su kuma taimaki 'ya'yan Haruna, maza, 'yan'uwansu, da yin hidimar Haikalin Ubangiji.

Karanta cikakken babi 1 Tar 23