Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 2:3-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. 'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela. Waɗannan uku Batshuwa Bakan'aniya, ita ce ta haifa masa su. Amma Er, ɗan farin Yahuza, mugu ne a gaban Ubangiji, don haka Ubangiji ya kashe shi.

4. Surukarsa Tamar, matar ɗansa kuma ta haifa masa Feresa da Zera. Yahuza yana da 'ya'ya maza biyar.

5. 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.

6. 'Ya'yan Zera, maza, su ne Zabdi da Etan, da Heman, da Kalkol, da Darda. Su biyar ke nan.

7. Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra'ila wahala a kan abin da aka haramta.

8. Etan yana da ɗa guda ɗaya, shi ne Azariya.

9. 'Ya'yan Hesruna, maza, waɗanda aka haifa masa, su ne Yerameyel, da Arama, da kuma Kalibu.

10. Arama shi ne mahaifin Amminadab. Amminadab kuma shi ne mahaifin Nashon, shugaban 'ya'yan Yahuza.

11. Nashon shi ne mahaifin Salmon. Salmon kuwa shi ne mahaifin Bo'aza.

12. Bo'aza kuma shi ne mahaifin Obida. Obida shi ne mahaifin Yesse.

13. Yesse shi ne mahaifin Eliyab ɗan farinsa, sa'an nan sai Abinadab da Shimeya,

14. da Netanel, da Raddai,

15. da Ozem, da Dawuda. Su 'ya'ya maza bakwai ke nan.

16. 'Yan'uwansu mata kuwa su ne Zeruya da Abigail.'Ya'yan Zeruya, maza, su ne Abishai, da Yowab, da Asahel, su uku ke nan.

17. Abigail ta haifi Amasa. Mahaifin Amasa shi ne Yeter daga zuriyar Isma'ilu.

18. Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa 'ya'ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi 'ya'ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon.

19. Sa'ad da Azuba ta rasu sai Kalibu ya auri Efrata wadda ta haifa masa Hur.

20. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuwa shi ne mahaifin Bezalel.

21. Bayan haka sai Hesruna ya shiga wurin 'yar Makir mahaifin Gileyad, wadda ya aura sa'ad da yake da shekara sittin da haihuwa. Ta haifa masa Segub.

22. Segub shi ne mahaifin Yayir wanda yake da birane ashirin da uku a ƙasar Gileyad.

Karanta cikakken babi 1 Tar 2