Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 15:12-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. ya ce musu, “Ku ne shugabanni na gidajen kakanninku, Lawiyawa. Sai ku tsarkake kanku da 'yan'uwanku domin ku iya kawo akwatin alkawarin Allah na Isra'ila a inda na shirya masa.

13. Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”

14. Sa'an nan firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji Allah na Isra'ila.

15. Lawiyawa fa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah a bisa sandunansa a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.

16. Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa 'yan'uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske.

17. Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berikiya daga cikin 'yan'uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kishi.

18. Daga cikin 'yan'uwansu, har yanzu aka zaɓi mataimakansu, wato Zakariya, da Ben, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Benaiya, da Ma'aseya, da Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da masu tsaron ƙofofi.

19. Haka aka zaɓi mawaƙa, wato Heman, da Asaf, da Etan don su buga kuge na tagulla.

20. Su Zakariya, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Ma'aseya, da Benaiya, su ne masu kaɗa molaye da murya a sama.

21. Su Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da Azaziya suke ja da garayu da murya ƙasa-ƙasa.

22. Kenaniya shugaban Lawiyawa shi ne yake bi da waƙoƙi domin shi gwani ne.

23. Berikiya da Elkana su ne masu tsaron ƙofa ta akwatin alkawari.

24. Sai Shebaniya, da Yehoshafat, da Netanel, da Amasai, da Zakariya, da Benaiya, da Eliyezer, firistoci, suka yi ta busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-edom da Yehiya su ne kuma masu tsaron ƙofar akwatin alkawari.

25. Haka Dawuda, da dattawan Isra'ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom.

26. Saboda Allah ya taimaki Lawiyawa waɗanda suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai.

27. Dawuda yana saye da kyakkyawar taguwa ta lilin tare da Lawiyawa duka waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, da mawaƙa, da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dawuda kuma ya sa falmaran ta lilin.

28. Da haka fa Isra'ilawa duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 15