Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 12:32-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Na kabilar Issaka akwai shugabanni ɗari biyu, waɗanda suka gane da halin da ake ciki, da abin da ya kamata Isra'ila ya yi. Su ne suke shugabancin 'yan'uwansu.

33. Na kabilar Zabaluna akwai mutum dubu hamsin (50,000) suna da kowane irin kayan yaƙi. Suka zo domin su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya.

34. Na kabilar Naftali akwai shugabannin sojoji dubu ɗaya (1,000) tare da sojoji dubu talatin da dubu bakwai (37,000) masu garkuwoyi da māsu.

35. Na kabilar Dan mutum dubu ashirin da takwas da ɗari shida (28,600).

36. Na kabilar Ashiru, sojoji dubu arba'in (40,000) suka fito da shirin yaƙi.

37. Kabilan gabashin Urdun, wato kabilar Ra'ubainu, da Gad, da rabin kabilar Manassa, su dubu ɗari da dubu ashirin ne (120,000), suna da kowane irin kayan yaƙi.

38. Duk waɗannan mayaƙa sun zo Hebron a shirye, da zuciya ɗaya don su naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka. Haka kuma dukan sauran Isra'ilawa suka goyi baya da zuciya ɗaya a naɗa Dawuda ya zama sarki.

39. Suka yi kwana uku tare da Dawuda, suka yi ta ci suna sha, gama 'yan garin sun shirya wata liyafa dominsu.

40. Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.

Karanta cikakken babi 1 Tar 12