Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 12:26-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Na kabilar Lawi akwai mutum dubu huɗu da ɗari shida (4,600).

27. Akwai kuma Yehoyada wanda shi ne shugaban gidan Haruna, yana da mutum dubu uku da ɗari bakwai (3,700).

28. Na dangin Zadok wanda yake jarumi, saurayi, akwai shugabannin sojoji ashirin da biyu.

29. Na kabilar Biliyaminu, wato kabilar Saul, akwai mutum dubu uku (3,000). (Har yanzu yawancin mutanen Biliyaminu ba su daina bin gidan Saul ba.)

30. Na kabilar Ifraimu akwai mutum dubu ashirin da ɗari takwas (20,800), jarumawa ne sosai, waɗanda suka shahara a danginsu.

31. Na rabin kabilar Manassa wajen yamma akwai mutum dubu goma sha takwas (18,000) waɗanda aka zaɓa domin su zo su naɗa Dawuda ya zama sarki.

32. Na kabilar Issaka akwai shugabanni ɗari biyu, waɗanda suka gane da halin da ake ciki, da abin da ya kamata Isra'ila ya yi. Su ne suke shugabancin 'yan'uwansu.

33. Na kabilar Zabaluna akwai mutum dubu hamsin (50,000) suna da kowane irin kayan yaƙi. Suka zo domin su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya.

34. Na kabilar Naftali akwai shugabannin sojoji dubu ɗaya (1,000) tare da sojoji dubu talatin da dubu bakwai (37,000) masu garkuwoyi da māsu.

35. Na kabilar Dan mutum dubu ashirin da takwas da ɗari shida (28,600).

36. Na kabilar Ashiru, sojoji dubu arba'in (40,000) suka fito da shirin yaƙi.

37. Kabilan gabashin Urdun, wato kabilar Ra'ubainu, da Gad, da rabin kabilar Manassa, su dubu ɗari da dubu ashirin ne (120,000), suna da kowane irin kayan yaƙi.

38. Duk waɗannan mayaƙa sun zo Hebron a shirye, da zuciya ɗaya don su naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka. Haka kuma dukan sauran Isra'ilawa suka goyi baya da zuciya ɗaya a naɗa Dawuda ya zama sarki.

39. Suka yi kwana uku tare da Dawuda, suka yi ta ci suna sha, gama 'yan garin sun shirya wata liyafa dominsu.

40. Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.

Karanta cikakken babi 1 Tar 12