Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 20:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai ya ce wa jakadun Ben-hadad, “Ku ce wa maigirma, sarki, dukan abin da ya nema a wurina da farko, zan yi, amma wannan na ƙarshe, ban zan iya yi ba.”Jakadun kuwa suka koma da wannan labari.

10. Ben-hadad kuwa ya sāke aikawa wurinsa ya ce, “Bari alloli su kashe ni idan ban kai mutane da yawa da za su hallaka Samariya ba.”

11. Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa'an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”

12. Da Ben-hadad ya ji wannan saƙo sa'ad da yake sha tare da sarakuna a sansani, sai ya ce wa mutanensa, “Kowa ya tsaya a wurinsa.” Sai kowa ya tsaya a wurinsa don yin yaƙi da birnin.

13. Ba da jimawa ba, sai ga annabi ya zo wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan babban taron sojoji? Zan ba da su a hannunka yau, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”

14. Ahab ya ce, “Wane ne zai yi jagorar yaƙin?”Annabin ya ce, “Ubangiji ya ce, sojoji matasa, wato na hakiman larduna, za su yi yaƙin.”Sarki ya ce, “Wa zai yi jagorar babbar rundunar?”Annabin ya ce, “Kai ne.”

15. Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa'an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra'ila dubu bakwai (7,000).

16. Suka tafi da tsakar rana sa'ad da Ben-hadad yake a buge da sha a sansani, shi da sarakuna talatin da biyu waɗanda suka taimake shi.

17. Samarin ne suka fara fita. Sai Ben-hadad ya aiki mutane, suka faɗa masa cewa, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”

18. Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”

19. Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra'ilawa kuma tana biye da su,

20. kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.

Karanta cikakken babi 1 Sar 20