Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 19:18-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai(7,000) na Isra'ila waɗanda ba su rusuna wa Ba'al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”

19. Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa.

20. Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.”Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”

21. Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 19