Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 19:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.

12. Bayan girgizar kuma, sai wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wutar. Bayan wutar sai ƙaramar murya.

13. Sa'ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”

14. Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”

15. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka juya zuwa jeji kusa da Dimashƙu, idan ka isa can, sai ka zuba wa Hazayel mai, ka keɓe shi, ya sama Sarkin Suriya,

16. da Yehu ɗan Nimshi, ka keɓe shi, ya zama Sarkin Isra'ila. Ka kuma zuba wa Elisha, ɗan Shafat na Abel-mehola, mai, ka keɓe shi, ya zama annabi a maimakonka.

17. Duk wanda zai tsere wa Hazayel, Yehu zai kashe shi. Wanda kuma ya tsere wa Yehu. Elisha zai kashe shi.

18. Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai(7,000) na Isra'ila waɗanda ba su rusuna wa Ba'al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”

19. Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 19