Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:37-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”

38. Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.

39. Sa'ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka rusuna suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”

40. Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba'al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.

41. Iliya kuwa ya ce wa Ahab, “Sai ka haura ka ci ka sha, gama akwai motsin sakowar ruwan sama.”

42. Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa.

43. Sa'an nan ya ce wa baransa, “Ka tafi ka duba wajen teku.”Baran kuwa ya tafi ya duba, ya komo ya ce, “Ban ga kome ba.”Sai ya ce, “Ka yi tafiya kana dubawa, har sau bakwai.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 18