Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:16-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.

17. Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne, wanda kake wahalar da Isra'ila?”

18. Iliya kuwa ya amsa ya ce, “Ban wahalar da Isra'ila ba, kai ne da tsohonka, gama kuna ƙin bin umarnan Ubangiji, kuna yi wa Ba'al sujada.

19. Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra'ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba'al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”

20. Sai Ahab ya aika wa dukan jama'ar Isra'ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel.

21. Iliya kuwa ya zo kusa da jama'a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba'al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.

22. Sa'an nan ya ce wa jama'a, “Ni kaɗai ne annabin Ubangiji da ya ragu, amma annabawan Ba'al ɗari huɗu ne da hamsin.

23. To, a ba mu bijimi biyu, su su zaɓi guda su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa a kan itacen wuta, amma kada su kunna masa wuta. Ni kuma zan shirya ɗaya bijimin, in shimfiɗa bisa itacen wuta ba kuwa zan kunna masa wuta ba.

24. Za ku yi kira ga sunan Ba'al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.”Jama'a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.

Karanta cikakken babi 1 Sar 18