Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 17:8-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya.

9. “Tashi ka tafi Zarefat ta Sidon, ka zauna a can. Ga shi, na umarci wata mace wadda mijinta ya rasu ta ciyar da kai.”

10. Sai ya tashi, ya tafi Zarefat. Sa'ad da ya isa ƙofar garin, sai ga wata wadda mijinta ya rasu tana tattara itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa in sha.”

11. Ta juya ta tafi don ta kawo masa ruwan sha ke nan, sai ya sāke kiranta, ya ce, “Ki kuma kawo mini ɗan abinci.”

12. Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”

13. Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini 'yar waina, ki kawo mini, sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki.

14. Gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Garin da yake a tukunyarki ba zai ƙare ba, man da yake a kurtunki kuma ba zai ƙare ba, sai ran da Ubangiji ya sa aka yi ruwan sama a ƙasar.’ ”

15. Ta tafi, ta yi yadda Iliya ya ce, dukansu kuwa suka sami isasshen abinci har kwanaki da yawa.

16. Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.

17. Bayan wannan sai ɗan macen, wato ɗan uwargijiyar gidan, ya yi ciwo. Ciwon kuwa ya tsananta har ransa ya fita.

18. Sai macen ta ce wa Iliya, “Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo don ka nuna wa Allah zunubina, ka zama sanadin mutuwar ɗana?”

19. Iliya ya ce mata, “Ki kawo mini ɗanki.” Ya karɓe shi daga wurinta, ya kai shi a bene inda yake kwana. Ya kwantar da shi a gadonsa.

20. Sa'an nan ya yi addu'a da gaske ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wa gwauruwan nan da nake zaune wurinta masifa, ka aukar wa ɗanta da ajali?”

21. Sa'an nan ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya kuma yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka sa ran yaron nan ya komo cikinsa.”

22. Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.

Karanta cikakken babi 1 Sar 17